Mene ne Kasuwar Bello?

  • Kasuwar Bello itace kasuwar Hausa ta farko akan yanar gizo dake tattara ‘yan kasuwa da sana’o’i a waje daya domin su samu kudi, tare da basu sababbin dabarun zamani na kasuwanci da gina tattalin arziki.

  • Kasuwar Bello na baiwa ‘yan kasuwa hanyoyin samun bayanai akan ko wani irin kaya dake China da Amurka da ma shiri na musamman domin sayo musu da aika musu har gida a Najeriya da Nijar.

  • Kasuwar Bello na baiwa kamfanoni shawarwarin hanyoyin bunkasa harkokinsu da fitar da kaya zuwa kasashen waje.

  • Kasuwar Bello na da shiri na musamman na nemar wa dalibai makarantu da ma baiwa matasa tallafin karatu zuwa kasashe daban-daban a duk fadin duniya.

  • Kasuwar Bello na koyawa kananan ‘yan kasuwa hanyoyi masu sauki na tallata sana’o’in su akan yanar gizo da neman cigaba.

  • Kasuwar Bello na koyar da harsunan kasashen waje ga duk wanda yake sha’awar tafiya kasuwanci.

  • Kasuwar Bello na bada shagunan yanar gizo kyauta ga duk wanda yake bukata da koya musu yadda ake samun kudi da su.