Ta Yaya Ake Jan Hankulan Jama’a a Kasuwar Bello?

Akwai hanyoyi da dama. Babbar hanya itace ka mayar da hankali wajen tallata abu daya a kowani talla, ba shagon ka ba. Ka dauki abu daya, ka yiwa kwastomomi bayanin sa dalla-dalla, ka nuna ka fahimce shi, sannan ka gaya wa jama’a dalilin da yasa ya kamata su saya a wajen ka. Kar ka bata lokacin ka tallar sunan shagon ka, a’a. Abunda zaka siyar shine zai jawo hankali mai bukata, kai kuma sai ka bar cikakkun bayanai yadda ya kamata a kan shafin.