Su Waye Suka Kafa Kasuwar Bello


Malamin kasuwanci da harsunan kasashen waje kuma dan jarida Bello Galadanchi Ph.D tare da dan kasuwa mai hada-hadar kafofin sadarwar zamani da harkokin noma Bello Ado Husseini ne suka kafa Kasuwar Bello.

A watan Fabrairun 2017 ne Bello da Bello suka hadu a karon farko, inda suka yi kokarin sayo kayan gona daga manoma daban-daban domin sayarwa a kasashen waje. Wannan aiki ya zo da kalubale sosai saboda dole sai an nemi lambar wayar manoma, an ziyarce su kafin a tantance ko amfanin gonarsu ya cancanci a aika kasashen waje. Wannan aiki da ya kamata ya share kwanaki uku ya kwashe sama da makonni biyu. A nan ne Bello da Bello suka yanke shawarar kafa mattatarar bayanai inda ba manoma kawai ba, har wasu ‘yan kasuwa da sana’o’i duk zasu iya buga bayanan su kuma su tallata hajjar su kullum, domin kawo wa jama’a sauki.