Mene ne muhimmancin hoto a talla?

Har abada dan adam baya gajiya da hotuna. Duk abunda ka fada, zamu iya tunanin siffar sa a zuciyar mu, ko da ba dai-dai bane. Amma shi hoto, yana baiwa jama’a hakikanin gaskiyar abunda yake faruwa. Idan kana so ka jawo hankulan jama’a, to ka ringa saka hoto mai ma’ana, kuma hoton yayi kyau. Hoto gangariya wanda aka dauka a gidan hoto na da matukar amfani wajen jawo hankulan jama’a ga sana’ar ka, saboda idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.